Brazil

Gwamnatin Brazil ta yi alkawalin aiwatar da sabbin sauye sauye

Masu zanga-zanga a kasar Brazil suna arangama da Jami'an tsaro  da ke harba masu hayaki mai sa hawaye
Masu zanga-zanga a kasar Brazil suna arangama da Jami'an tsaro da ke harba masu hayaki mai sa hawaye Reuters

Shugabar Kasar Brazil, Dilma Roussef, ta gabatar da wani shirin gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a don amincewa da sabbin sauye sauye, sakamakon zanga zangar da aka kwashe kwanaki ana yi a kasar. Roussef ta yi alkawarin bunkasa harkokin kasuwanci da kuma mayar da hankali kan samar da ilimi da kiwon lafiya.

Talla

Taron Gwamnonin kasar da Magadan Gari sun amince da shirin, amma wasu masu zanga zangar sun ce ba su gamsu ba kuma zasu ci gaba da bore.

Tun fara wasannin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya ne mutanen Brazil suka bazama saman tituna suna zanga-zanga tare da arangama da Jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI