Brazil

An samu asarar rayukan mutane akalla 7 a tarzomar birnin Rio

Masu zanga-zanga a kasar Brazil
Masu zanga-zanga a kasar Brazil Reuters/路透社

Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon wani artabu da aka yi da makamai a wata unguwa ta marasa galihu da ke wajen birnin Rio de Janeru na kasar Brazil a yau talata.

Talla

Bayanai na nuni da cewa, rikici ya barke tsakanin jami’am tsaro da masu gudanar da zanga-zanga, lokacin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka soma farfasa shagunan jama’a domin kwashe kayayyakinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.