Amurka-Afrika

Mandela kamar darasi ne ga shugabannin duniya, inji Obama

Ziyarar Shugaban Amurka Barack Obama a kasar Afrika ta Kudu.
Ziyarar Shugaban Amurka Barack Obama a kasar Afrika ta Kudu. REUTERS/ Gary Cameron

Shugaban Amurka Barack Obama zai gana da iyalan Tsohon shugaba Nelson Mandela a ziyarar da ya kai a kasar Afrika ta kudu. Sai dai babu tabbaci ko Obama zai gana da Mandela wanda ke kwance a gadon Asibiti cikin mayuyacin hali. Tuni Barack Obama ya bayyana Mandela a matsayin jaruminsa wanda ya ke alfahari da shi.

Talla

Shugaba Obama ya fara ziyara ne a kasashen Afrika guda uku a ranar Laraba inda ya fara da Senegal kafin ya gana da shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma a birnin Pretoria.

Huldar kasuwanci da tattalin arziki su ne batutuwan da suka mamaye ziyarar Obama a kasashen na Afrika.

Tun a ranar 8 ga watan Juni ne aka kwantar da Mandela mai shekaru 94 a gadon Asibiti, sakamakon lashin lafiyar huhu da ya kwashe shekaru yana jinya.

Mutanen Afrika ta kudu dai sun shiga damuwa game da makomar tsohon shugabansu wanda ya yi yaki da wariya a zamanin mulkin fararen fata a kasar.

Amma tsohuwar matar shi Winnie Madikizela-Mandela tace tsohon shugaban ya fara samun sauki fiye da kwanakin baya da aka ruwaito rashin lafiyar shi ta tsananta.

A lokacin da ya ke zantawa da matasan Afrika, shugaba Obama yace Nelson Mandela ya zama darasi ga shugabannin duniya, musamman shugabannin kasashen Afrika da ke fuskantar kalubalen kubutar da Nahiyar daga dimbin matsalolin da ke addabar mutanen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.