Amurka

An yi bikin auren Madigo a California

Masoyan juna Sandy Stier da Kris Perry da suka gudanar da bukin aurensu na 'Yan madigo a California.
Masoyan juna Sandy Stier da Kris Perry da suka gudanar da bukin aurensu na 'Yan madigo a California. REUTERS/Stephen Lam

Wasu ‘Yan madigo sun gudanar da bukin aurensu a California a karon farko Bayan Koton koli ta janye haramta auren jinsi. mutane da dama ne suka halarci bikin auren a San Francisco na ‘Yan madigon guda biyu, Kristin Perry da Sandy Stier.

Talla

Masoyan sun yi musayar zobe tare yin rantsuwar ci gaba da kasancewa da juna har abada.

“Mun dade muna jiran wannan ranar” inji Stier bayan kammala bikin, wanda shi ne na farko tun a shekaraer 2008 da mahukuntan California suka jingine dokar.

Bikin auren madigon  na zuwa sa’o’I kalilan da kotun San Francisco ta janye haramcin auren jinsi.

Rahotanni sun ce ‘Yan madigo da dama ne da 'Yan Luwadi yanzu suke yin tururuwa domin shirin kulla aure bayan gudanar da auren farko na Perry da Stier.

Perry da Stier sun ce sun dade suna soyayya da juna tsawon shekaru 14, suna masu bayyana fatar zasu ci gaba da rayuwa cikin soyayya da kaunar juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.