Pakistan-Afghanistan

Rayuka da dama sun salwanta a Pakistan yayin da David Cameron ke ziyara a kasar

Daya daga cikin ahre haren da ya yi sandaiyar mutuwar mutane sama da 50 a Pakistan
Daya daga cikin ahre haren da ya yi sandaiyar mutuwar mutane sama da 50 a Pakistan

Firaministan kasar Pakistan, Nawaz Sharif tare da takwaransa na Birtaniya David Cameron sun kara jaddada dankwan dangartakar dake tsakaninsu tare shan alwashin maido da zaman lafiya a kasar Afghanistan ta hanyar yaki da ta’addanci da tsatsauran ra’ayi.

Talla

A lokacin ziyarar da ya kai kasar ya bayyana cewa kawayen kasar Pakistan kwaye ne ga kasar Birtaniya, haka kuma makiyan Pakistan makiya ne ga Birtaniya.

Cameron dai ya yi tattaki ne zuwa kasar ta Pakistan domin marawa yunkurin da kasashen duniya ke yi na maido da zaman lafiya a kasar Afgahnistan wacce makwabciya ce ga Pakistan inda ya yi kira da a tashi tsaye wajen yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa za su tsaya kafada da kafada domin yaki da ayyukan ta’addanci da kuma tsatsauran ra’ayi.

A daya bangaren kuwa, Firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya tabbatarwa da Cameron cewa sun daura aniyar ganin cewa sun bi sahun samar da daurarran zaman lafiya a kasar Afghanistan.

Ya kuma kara cewa samar da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan zai bawa masu gudun hijra dake zaune a nan Pakistan damar komawa kasarsu a mutunce.

Sai dai a dai dai lokacin da Cameron ke wannan ziyara wasu hare hare da aka kai a sassa daban daban na kasar sun hallaka akalla mutane sama da 50.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.