Brazil

Paparoma Francis na ziyara a garin Aparecida na kasar Brazil

Aparecida, wuri mai muhimmanci ga mabiya darikar Katolika
Aparecida, wuri mai muhimmanci ga mabiya darikar Katolika REUTERS/Nacho Doce

Paparoma Francis, wanda ke ci gaba da ziyarar aiki a kasar Brazil, ya bukaci matasa a wannan zamani da su kaucewa son kudi da kuma son mulki, saboda da a cewarsa su ne abubuwan da ke ruda mutum har ma ya kaucewa hanyar bautawa Ubangijinsa.

Talla

Paparoma wanda ke gudanar da ziyara ta farko a matsayinsa na shugaban Cocin Katolika a kasar ta Brazil, a yau laraba ya kai ziyarar ne a Apare-cida, yankin da mabiya darikar katolika ke dauka da matukar muhimmanci, inda ya gabatar da jawabi a gaban dubban matasa..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.