Brazil

Gwamnatin Brazil ta ware kudi domin gyara birnin Sao Paulo

Masu Zanga-zangar adawa da gwamnatin Brazil
Masu Zanga-zangar adawa da gwamnatin Brazil Reuters

Shugabar kasar Brazil da ke kokarin shawo kan matsalar yajin aiki da kuma tarzoma a kasar, ta sanar da ware dalar Amurka miliyaa dubu uku da 600 domin gina birnin Sao paolo wanda shi ne cibiyar kasuwancin kasar. A karkashin wannan shiri, gwamnati za ta gina sabbin hanyoyin mota da kuma fasalta birnin, inda ayyukan a tunanin gwamnatin kasar za su kara kwantar da hankulan jama’a da kuma samar da sabbin gurabobin ayyukan yi.