Afrika

Kungiyar BRICS na tattaunawa da manyan ‘Yan kasuwan Afrika

Shugabannin kasashen da suka hada kungiyar BRICS
Shugabannin kasashen da suka hada kungiyar BRICS REUTERS/Rogan Ward

Shugaban ‘Yan kasuwan da suka fito daga kasashen dake kungiyar BRICS, wato Brazil, Russia, India, China da Afrika ta kudu, na cigaba da gudanar da taron su tare da ‘yan kasuwan da suka fito daga Afrika, domin bunkasa harkokin kasuwanci da ciniki a tsakanin su.

Talla

Shugaban tawagar ‘yan kasuwan China, Ma Zehua, ya bayyana cewar, har yanzu Gwamnatin su na da kwarin gwiwar ganin sun kafa Bankin da zai kalubalanci bankin duniya.

Jami’in ya ce, bankin zai taka rawa sosai wajen tallafawa ‘yan kasuwar kasashen, da ma gwamnatocin su wajen kasuwanci da zuba jari.

Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma da ya bude taron, ya bukaci ‘yan kasuwan da su zuba jari wajen bunkasa kayan more rayuwa a nahiyar Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI