Faransa

Hollande na neman hadin kan kasashen Nahiyar Turai akan kai hari Syria

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Srdjan Zivulovic

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande na ci gaba da neman hadin kan kasashen Nahiyar Turai akan irin matakin da za su dauka akan kasar Syria, yayin da Ministocin harkokin kasashen wajen nahiyar ke shirin gudanar da wani taro a karshen mako mai zuwa.

Talla

Shugaban ya yi kira ga kasashen ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a yau Talata.

“Ya zama dole kasashen nahiyar Turai su hada kansu akan wannan batu, Faransa dai ta dauki matsaya.” Inji Hollande.

A cewar Hollande a duk lokacin da aka yi amfani da makamai masu guba, kuma aka sanar da duniya tare da hujja ya kamata a kai dauki.

“Wannan dauki ya kamata ya zo ne daga kasashen duniya.” Hollande ya ce.

Wannan kira na Hollande na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar Amurka ke aikawa da jiragen ruwan yakinta a gabar Tekun Gabas ta Tsakiya.

Wani jami’in tsaron kasar Amurka ya ce kasancewarsu a yankin shine babban batu, ya kuma kara da cewa ba a basu umurnin su kai hari ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.