Amurka

‘Yan sandan Amurka na kokarin gano dalilin kai harin Washington

Aaron Alexis, mutumin da ake zargi da kashe mutane 12 a wani sansanin sojin kasar Amurka a Washington
Aaron Alexis, mutumin da ake zargi da kashe mutane 12 a wani sansanin sojin kasar Amurka a Washington REUTERS/Fort Worth Police Department/Handout via Reuters

Masu bincike na ci gaba da kokarin gano dalilin da ya sa wani tsohon sojan ruwan kasar Amurka, Aaron Alexis ya bude wuta akan mutane a jiya Litinin a wani sansanin sojin ruwan kasar Amurka dake birnin Washington DC, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 kana wasu da dama suka jikkata.

Talla

Da sanyin safiyar yau ne hkumomin kasar Amurka suka bayyana sunan Alexis a matsayin wanda ya kai harin, wanda ainihi mazaunin Jihar Texas ne.

Ya kuma yi aiki da rundunar mayakan ruwan kasar Amurka daga shekarar 2007 zuwa 2011 kamin nan ya koma kamfanin sarrafa nau’rar zamani na Hewlett- Packard.

Yanzu haka jami’an tsaro sun fitar da sanarwar cewa jama’ar kasar su taimaka wajen samar da bayanan da za su sa a gano musabbaib da ya sa Alexis, dan shekaru 34 ya aikata wannan aika-aika.

“Komai kankantan bayani game da Alexis, muna bukatar a tuntibe mu.” In ji Mataimakin Darektan hukumar bincike ta FBI, Valerie Parlave.

Harin da Alexis ya kai har ila yau ya raunata mutane 14 kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Bayani na nuna cewa a lokacin da ya ke aikin sojin kasar ta Amurka an taba samun shi da laifukan rashin da’a wanda hakan ya sa aka hukunta shi a lokacin.

Akalla mutane 3,000 ke aiki a sansanin sojin ruwan kasar na Amurka wanda ke cike da dumbin tarihi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.