Isra'ila-Felesdinu

Isra’ila ta soki jekadun Turai game da tallafin Falasdinawa

Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun

Kasar Isra’ila ta zargi Jakadaun kungiyar kasashen Turai da haifar da rudani wajen raba kayan agaji ga Falasdinawa a Gabar Yamma da kogin Jordan, abinda ya sa jami’an tsaro suka ci zarafin su. Ma’aikatar harkokin wajen kasar, tace gwamnatoci na tura jakadun su don kulla hulda ne ba wai tayar da hankali ba, inda ta bukaci Jakadun da su yi bayani akai.

Talla

Idan dai ba’a manta ba, sojojin Israila sun ci zarafin Jakadun da suka isa Yankunan Falasdinawa, abinda ya kai ga ture ‘Yar majalisar Faransa har sai da ta fadi a kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.