Iran

Iran ta yi fatan bude sabon babin dangantaka da sauran kasashe duniya

Sabon shuagban kasar Iran, Hassan Rouhani
Sabon shuagban kasar Iran, Hassan Rouhani Reuters/Adrees Latif

Bayan tattaunawar ta kwanaki biyu, Iran ta ce tana fatan bude wani sabon babin dangantaka, tsakanin ta da sauran kasashen duniya. Tuni gwamnatin Amurka ta yaba da wannan matakin, inda ta ce hakan na nuna cewa Iran da aske ta ke yi.  

Talla

Ita ma kasar Jamus ta bayyana fatan tattaunawar za ta samar da mafita cikin ruwan sanyi.

Sai dai kuma Rasha ta ce yanzu ba lokaci ne da za a fara guda kan batun ba.

Babbar jami’ar Diplomasiyyar kungiyar Taraiyyar Turai ta EU Catherine Aston ta shaida wa manema labaru cewa za a ci gaba da tattaunawa kan batun a ranakun bakwai da takwas ga watan Nuwamba.

Dama kasasshen Amurka, Faransa, Birtaniya, China, Rasha da Jamus, sun yi ta tattaunawa da Iran, don neman ta dakatar da shirin ta na kera makaman Nukiliya, da ake ganin ta shafe shekaru tana yi.

Tun a baya Iran ta yi ikararin cewa shirin nata na samar da makamashin wutar lantarki ne ba na makami ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.