Amurka

Amurkawa sun nemi a takaita ayyukan leken asiri a kasar

Wani mutum, da ke rajin ganin Amurka ta dakatar da ayyukan leken asiri
Wani mutum, da ke rajin ganin Amurka ta dakatar da ayyukan leken asiri Allison Shelley/Getty Images/AFP

Dimbin jama’a ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Washington na kasar Amurka, inda suke neman hukumomin kasar su samar da sabbin dokoki da za su taikaita ayyukan leken asiri da hukumar tsaron kasar wato NSA ke yi, kan jama’a a ciki da wajen kasar. Masu zanga-zangar dai sun gabatarwa Majalisar dokokin kasar da bukata mai dauke da sa hannun mutane akalla dubu 575 dukkaninsu Amurkawa, da ke neman ganin hukumar ta samar da doka dangane da ayyukan leken arsirin wannan hukumar, wadanda a yau suka jefa kasar a cikin hali na zargi daga manyan kasashe aminanta kamar Jamus da kuma Faransa.