Saudiya

Saudiyya ta yiwa wani dan Pakistan haddi, kan safarar Kwayoyi

Sarkin makka Adballah bin Abdul'aziz
Sarkin makka Adballah bin Abdul'aziz

Hukumomi a Saudi Arebiya sun aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar fille Kan wani dan kasar Pakistan akan samun sa da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Talla

Ministan harkokin cikin Gida na Saudiyya ya ce an kama Ja’afar Ghulam Ali da laifin safarar Sinadarin Heroin ne a gabashin Lardin Qatif aka kuma gurfanar da shi.

Fille Kan wanann mutumin dai ya kai ga samun mutane 71 da aka yankewa irin wannan hukuncin a Saudiyya a wannan Shekarar kurum.

A Shekarar 2012 ma kasar mai bin shara’ar Musulunci tsantsa, ta aiwatar da haddi ga mutane 76, amma wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana cewar adadin mutanen da aka yankewa hukuncin kisa a Saudi Arebiya duka duka 69 ne.

Laifukan Fyade da kisan Kai da ridda, da fashi da Makami da safarar miyagun kwayoyi, duka hukuncin su kisa ne a kasar Saudi Arebiya a karkashin Dokar shara’ar Musulunci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.