Philippines

MDD ta fitar adadin wadanda suka mutu a Philippines

Wasu dauke da gawar wani da guguwar ta halaka a Philippines
Wasu dauke da gawar wani da guguwar ta halaka a Philippines REUTERS/Romeo Ranoco

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na ta adadin mutanen da suka mutu sanadiyar Guguwar Haiyan da ta mamaye yankin Philippines inda ta ce yawan wadanda suka ya kai kusan 4,460. 

Talla

Sai dai hukumar dake kula dake kare aukuwar bala’I a kasar ta musanta wannan adadi inda ta ce adadin ba wuce mutane 2,460.

Izuwa ana ci gaba da aikewa da kayyayakin tallafi daga kasashen duniya daban daban inda wani katafaren jirgin ruwan Amurka ya isa gabat tekun kasar a yammacin jiya yayin da Birtaniya ta aika da na ta jirage dauke da kayyaykin masarufi.

Tun a karshen makon da ya gabata ne guguwa Haiyan ta abkawa yankin na Philippines lamarin da tsunduma kasar cikin halin da take ciki a yanzu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.