Amurka

Obama ya nuna takaicinsa game da rushewar tsarin kiwon lafiya

Shugaban kaar Amurka, Barack Obama
Shugaban kaar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda ke ya kare shirinsa na inshorar kiwon lafiya da ke ci gaba da fuskantar suka daga abokannin hamayyarsa na siyasa dake jam’iyyar Republican.

Talla

Da farko dai shugaban na Amurka ya ce yana sane da korafe korafen da wasu daga cikin al’ummar kasar ke gabatarwa dangane da wannan shiri.

Sai dai kamar yadda Obama ya ci gaba da cewa, har yanzu milyoyin mutane a kasar za su ci gaba da cin moriyar shirin har na tsawon shekara daya anan gaba duk da cewa a karkashin dokokin kasar ba su cika ka’idojin da ke ba su damar amfana da insharar lafiya ba.

Kalaman na Obama dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu alkalumman jin ra’ayin jama’a ke nuni da cewa farin jininsa ya yi kasa matuka sakamakon dagewa kan wannan shiri na inshorar lafiya.

A daya bangare kuwa shugaban na Amurka, ya bukaci Majalisun dokokin kasar da su dakatar da daukar sabbin takunkumai a kan kasar Iran, domin a cewarsa za su iya kawo cikas ga tattaunawa dangane da batun nukilyar kasar ta Iran.

Har ila yau wasu rahotanni na cewa Amurka na shirin sakowa Iran dala milyan 45, wasu kadan daga cikin bilyoyin kudade da kadarorin kasar da ta kwace tsawon shekaru.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.