Kuwait

Shugabannin Afrika da Larabawa sun kammala taro a Kuwait

Sakin kasar Kuwait Sheikh Sabah al Ahmed al Sabah kusa da Sarki Abdallah na Jordan tare da shugabannin kasashen Afrika da na Larabawa a zauren taron da suka gudanar karo na uku.
Sakin kasar Kuwait Sheikh Sabah al Ahmed al Sabah kusa da Sarki Abdallah na Jordan tare da shugabannin kasashen Afrika da na Larabawa a zauren taron da suka gudanar karo na uku. REUTERS/Stringer

Shugabannin kasashen Larabawa da na Afrika sun kammala taronsu na kwanaki biyu a Kuwait inda suka amince su karfafa huldar diplomasiya da kasuwanci da kuma hada hannu domin yaki da Ta’addanci.

Talla

Shugabannin kasashen na Larabawa da Afrika sun yi nazari ne game da inganta huldar kasuwanci tare da neman kulla wata yarjejeniya ta taimakawa kai karkashin wani kudiri da suka amince shekaru uku da suka gabata a kasar Libya.

Tun bude taron a Kuwait, Sarki Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya yi alkawalin ware kudi Dala Biliyan daya don saka jari a kasashen Afrika da kuma tallafi ga kasashe masu karamin karfi tare da hadin guiwar Bankin duniya.

Shugabannin kasashe 71 ne suka halarci taron daga kasashen Afrika da Larabawa, kuma wannan ne taron farko tun wanda aka taba gudanarwa a kasar Libya a 2010 kafin barkewar zanga-zanga a kasashen Larabawa.

Akwai arziki a Afrika musamman noma da albarkatun kasa da makamashi amma akwai gazawa wajen sarrafa arzikin, lamarin da masana suke ganin ana iya samun sauyin tattalin arziki idan har bangarorin biyu suka hada kai.

Sai dai kuma babu wani yunkuri a zaman Taron na Afrika da Larawaba domin samar da kasuwa ta bai daya a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.