Masar

Harin bom kan ofishin 'yan sandan Masar ya kashe mutane 15

Ofishin 'yan sandan da aka kai hari a Mansoura dake Masar
Ofishin 'yan sandan da aka kai hari a Mansoura dake Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Wani hari da aka kai kan babban ofishin ‘yan sandan kasar Masar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15, lamarin da ya zamanto mafi muni cikin hare haren da aka kai tun bayan kawar da gwamnatin Mohammed Morsi. 

Talla

Harin an kai shine a yankin Mansoura dake birnin Alkahira a Arewacin kasar wanda ake zargin magoya bayan ‘yan kungiyar ‘Yan uwa musulmi da kaiwa.

Sai dai tuni kungiyar ta yi Allah wadai da harin yayin da wasu ke cewa masu tsatsauran kishin Islama dake kai hari a yankin Sinai ne suka kai harin.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Masar ta ce mutane 12 daga cikin wadanda suka mutu ‘yan sanda ne.

Akalla mutane sama da 1000 suka rasa rayukansu a rikicin siyasar na kwana kwana nan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.