Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar Abinci Ta Duniya na fuskantar gibin kudin tafiyar da ayyukanta

Yara marayu karkashin kulawar Hukumar Abionci ta Duniya a Koriya ta Arewa
Yara marayu karkashin kulawar Hukumar Abionci ta Duniya a Koriya ta Arewa Wfp.org
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta katse tallafin abincin da take bai wa wasu kasashen duniya, saboda gibin dala bilyan guda da hukumar ta samu a cikin kasafin kudadenta.

Talla

Daraktan hukumar, Ertharin Cousin, ta ce sakamakon raguwar kudaden ya sa sun zabtare taimakon da ya kamata su bai wa kasashen Haiti, Niger, Mali da Kenya.

Jami’ar hukumar ta ce ayyukansu na dada fadada, sakamakon karuwar mabukata musamman a Syria inda take neman ciyar da mutane sama da miliyan hudu akan kudi dala miliyan 40, yayin da kudaden ta na raguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.