Faransa

Bankin IMF ya bayyana amincewa da Christine Lagarde

Shugabar asusun lamani na duniya IMF, Christine Lagarde.
Shugabar asusun lamani na duniya IMF, Christine Lagarde. REUTERS/Ruben Sprich

Asusun bada lamuni na Duniya ya bayyana cikaken goyan bayansa kan shugabar gudanarwar Asusun Christine Lagarde, duk da tambayoyin da akayi mata dangane da cin hanci a Faransa.Mai magan da yawun asusun, Gerry Rice, yace anyi cikaken bayani ga hukumar gudanarwar akan matsalar, kuma ya bayyana goyan bayan sa kan Christine Lagarde, na cigaba da gudanar da ayyukan ta.Masu gabatar da kara a Faransa, sun yiwa Lagarde tambayoyi ranar 31 ga watan Janairu da ya gabata, a wata kotu ta musamman, saboda rawar da ta taka wajen yafewa wani Dan kasuwa mai suna Bernard Tapie, kudin da suka kai Euro miliyan 400, lokacin da take rike da mukamin ministan kudin kasar.Tuni aka samu wasu mutane biyar da laifi a badakalar, cikin su harda wani babban jami’in da ke aiki da Lagarde.