WHO

Gurbataccen iska yana kisan Al’umma a duniya

gurbatar yanayi a China
gurbatar yanayi a China ©REUTERS/Aly Song

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace kimanin mutane milyan 7 ne suka mutu sakamakon matsalar gurbatewar iska, musamman hayakin da ke fitowa daga injina da rishon dafa abinci, wanda har yanzu ke barazana ga lafiyar Dan Adam.

Talla

Rahoton na WHO yace hayakin risho na dafa abinci ya fi zama barazana ga lafiyar al’umma. Kuma matsalar ta shafi kasashe masu tasowa da manyan kasashe.

An bayyana cewa matsalar na haifar da cutuka da dama da ke kisan al’umma da suka hada da mutuwar jiki da ciwon zuciya da cutar sankarar makoshi da wasu cutuka da ake haihuwar jarirai da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.