Rasha-Ukraine-NATO

NATO ta nuna yadda Rasha ta jibge dakaru a Ukraine

Sakataren harakokin wajen Ukraine Andriy Deshchytsia da  Anders Fogh Rasmussen na NATO
Sakataren harakokin wajen Ukraine Andriy Deshchytsia da Anders Fogh Rasmussen na NATO REUTERS/Francois Lenoir

Kungiyar kasashen tsaro ta NATO ko kuma OTAN, ta fitar da wasu hotuna da ke nuna yadda kasar Rasha, ta jibge dakarunta kusan dubu arba’in a kan iyakar kasar da Ukraine, lamarin da kungiyar ta kwatanta shi a matsayin barazana ga birnin Kiev.

Talla

Kungiyar NATO ko OTAN ta yi kiyasin akalla dakarun Rasha dubu Talatin da biyar zuwa dubu arba’in aka jibge a kan iyakar ta Ukraine, tare da tankuna da sauran nau’ukan motocin yaki.

A cewar wani babban daraktan kungiyar, akwai yiwuwar wadannan dakaru su iya fadawa cikin kasar ta Ukraine da zaran an ba su oda.

Hotunan, wadanda aka dauka tsakanin watan Maris zuwa Afrilu ta hanyar tauraron dan adam, sun nuna sasanonin soji da dama a kan iyakar.

Daya daga cikin hotunan har ila yau ya nuna jirage sama masu tashin angulu guda 21, kuma bayanai na nuna cewa, ganin yadda sojin ba su batar da kama, hakan na nuna cewa suna so a gansu.

Wannan kuma na faruwa ne a daidai lokaci da hukumomin Rasha ke barazanar katse samar da iskan gas ga kasar Ukraine, inda ta nemi a biya ta wasu basukan da ta ke bin Ukraine na cinikayyar gas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.