Korea ta Kudu

Matukin jirgin Koriya ya kare kansa kan hadarin da ya auku

Matukin jirgin ruwan Koriya ta Kudu, Kyaftin Lee Joon- Seon (tsakiya) yayin da 'yan sanda suka tisa keyarsa
Matukin jirgin ruwan Koriya ta Kudu, Kyaftin Lee Joon- Seon (tsakiya) yayin da 'yan sanda suka tisa keyarsa REUTERS/Yonhap

Matukin jirgin ruwan kasar Koriya ta Kudu, Kyaftin Lee Joon- Seok, ya nemi gafara daga ‘yan kasar bayan da jirgin da yake jagoranta ya nutse dauke da mutane sama da 400. Jirgin ya jirkice ne kwanaki uku da suka gabata, koda yake an ceto akalla mutane sama da 100 yayin da wasu fiye da 200 suka bata.

Talla

Baya ga haka Joon- Seok ya kuma kare kansa game da zargin shi da ake yi wajen ba da odar jinkirta kwashe mutane inda ya ce ya yi hakan ne domin ya kare lafiyarsu.

A cewarsa, a lokacin da jirgin ya samu matsala babu wani jirgi a kusa da zai taimaka wajen kwashesu, lamari da ya sa ya ba da a dakata kadan, inda daga baya jirgin ya nutse.

Wanna kuma na faruwa ne a daidai lokacin da kwararru a fannin ninkaya suka gano wasu gawawwaki a cikin jirgin dake kasan ruwa.

Mafi yawan fasinjojin dake ciki jirgin dalibai ne dake hanyarus ta zuwa hutu tare da malamansu na makaranta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.