Rasha-Ukraine-Amurka

Dakarun Ukraine sun kaddamar da hare hare kan ‘yan a ware

Dakarun Ukraine a lokacin da suke kai hari kan 'yan a ware gabashin kasar
Dakarun Ukraine a lokacin da suke kai hari kan 'yan a ware gabashin kasar REUTERS/Gleb Garanich

Dakarun kasar Ukraine, sun kaddamar da wani hari kan ‘yan tawayen da suka sake karbe garuruwan dake Gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar, inda shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi kakkausan suka game da harin.

Talla

Putin ya kuma kara da cewa hakan zai haifar da wata makoma.

Wannan mataki ya sa farashin man fetur ya tashin goron zabi bisa la’akkari da matakin da Rasha ta yi barazanar dauka a baya kan kasar ta Ukraine.

Rahotanni sun ce an tankuna yaki suna dosar Slavyanska, garin da ‘yan a ware suka mamaye tun a tsakiyar watannan na Aprilu, yayin da ake ta jin karar bindigogi.

“A lokacin wannan arangama, akalla an kashe ‘yan tadda mutum biyar, sannan an lalata shingen bincike guda uku.” Inji ma’aikatar cikin gidan kasar ta Ukraine.

Wannan shine rikici mafi muni da ya auku tun bayan yarjejeniyar da aka saka a hanu akai kan kawo karshen rikici a gabashin kasar.

A karshen makon da ya gabata Amurka, Rasha da Ukraine tare da kungiyar tarayyar turai suka saka hanu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin gabashin Ukraine, shirin da bai haifar dad a mai ido ba.

Putin har ila yau, ya kwatanta wannan rikici a matsayin babban laifi.

“Idan har hukumomin Kiev sun yanke shawarar fara yin amfani da dakaru akan ‘yan kasarta, lallai wannan babban laifi ne.”

A kuma daidai wannan lokaci, rahotanni na nuna cewa Rasha na duba yiwuwar mayar da martani ta hanyar yin amfani da dakarunta da ta jibge a kan iyakar kasar Ukraine.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.