Rasha-Ukraine

Ukraine ta gargadi Rasha

Dakarun Ukraine suna musayar wuta da Masu kishin Rasha a Slaviansk.
Dakarun Ukraine suna musayar wuta da Masu kishin Rasha a Slaviansk. REUTERS/Gleb Garanich

Kasar Rasha ta aika da rundunar soji a yankunanta da ke kan iyaka da kasar Ukraine, a wani mataki na kokarin mayar da martani ga hare haren da Ukraine ta kaddamar akan masu kishin Rasha a yankin gabaci. Kasar Ukraine ta yi kira ga Rasha ta dai na yin kazanlandan ga harakokin da suka shafi al'amurranta.

Talla

A jiya Alhamis ne dakarun Sojin Ukraine suka kaddamar da yaki akan 'Yan aware masu kishin Rasha domin karbe ikon wasu biranen yankin gabacin kasar da 'Yan awaren suka kwace, matakin da kuma shugaba Putin na Rasha yace ba zai haifar da da mai ido ba.

Wannan dai wata barazanar yaki ce tsakanin kasashen biyu na tsohuwar daular Soviet.

Yanzu haka kuma Rasha ta bayar da umurnin a gudanar da atisayen soji a iyakokinta da Ukraine domin mayar da martani ga hare haren da Ukraine ta kaddamar akan 'Yan tawaye.

A cikin sanarwar da Rasha ta fitar, Ministan tsaronta Sergei Shoigu yace daga yau zasu ci gaba da horar da bataliyar soji a yankunan kudanci da yammaci da ke kan iyaka da Ukraine.

Sai dai kuma Tuni kungiyar tsaro ta NATO ta aika da dakarunta kimanin 40,000 akan iyakokin kasashen biyu domin kare duk wata barazana daga Rasha.

Rasha kuma tace tana kokarin kare rayukan mutanen yankin gabaci ne da ke ra'ayinta.

Rikicin Ukraine dai ya jefa kasashen yammaci da gwamnatin kasar ke ra'ayi cikin duhu, saboda duk matakin da zasu dauka akan Rasha na iya shafar tattalin arzikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.