Abdullah da Ghani na shirin zuwa zabe a zagaye na biyu

Wasu jami'an zabe a Afghanistan
Wasu jami'an zabe a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani

Rahotanni daga kasar Afghanistan na nuna cewa, za a sake zaben shugaban kasar a zagaye na biyu, bayan da ‘yan takarar suka gaza samun kashi 50 na kuri’un da aka kada a zaben kasar da aka gudanar a makwon da ya gabata.

Talla

Sakamakon farko na zaben, ya nuna cewa tsohon ministan wajen harkokin wajen kasar Abdullah Abdullah, ya kashi 44.9 na kuri’un da aka kada yayin da abokin hamayyarsa Ashraf Ghani ya samu kashi 31.5, lamarin da zai tilasta zuwa zagaye na biyu a zaben.

Dama hukumar zaben kasar ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu mai zuwa a matsayi ranar ad za a sake zabe a zagaye na biyu muddin ba a samu wanda ya lashe kashi 50 na kuri’u ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.