WHO

An samu raguwar mutuwar mata a wajen haihuwa

Wata Asibitinin kula da masu juna biyu a Habasha
Wata Asibitinin kula da masu juna biyu a Habasha REUTERS/Saul Loeb/Pool

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace an samu gagarumar nasara wajen raguwar yawan mata da yara da ke mutuwa a lokacin haihuwa. Wasu sabbin alkaluma da hukumar ta fitar an bayyana cewa an sami raguwar mutuwan matan da kashi 45 cikin 100.

Talla

Marleen Temmerman da ke shugabantar sashen haihuwa a hukumar ta WHO tace duk da wannan ci gaban da aka samu dole a tashi tsaye domin kawar da wannan matsalar baki daya, tare da jaddada cewar akwai jan aiki nan gaba saboda yadda mace guda ke mutuwa a kasa da mintuna biyu a lokacin haihuwa.

Jami’ar ta bayyana kasashe masu tasowa da kuma kasashe na kudu da sahara a matsayin yankunan da suka fi fuskantar matsalar mutuwa a yayin haihuwa sai dai kuma duk da haka akwai wasu kasashen Afrika da suka yi nasara wajen rage wannnan matsala a shekaru 23 da suka gabata a cewar rahoton WHO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.