Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar Lafiya ta bayyana dalilan faruwar cututuka ga matasa

Shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya Margaret Chan
Shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya Margaret Chan 照片来源:路透社REUTERS/Valentin Flauraud

Wani binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta gudanar, ya gano cewa koma-bayan da mutane ke samu a rayuwa, na kan gaba wajen haddasa cututuka da ma nakasa ga matasa. Hukumar ta kuma ce kashe kai na matsayi na 3, a jerin dalilan da ke sanadiyyar mutuwa a tsakanin matasa.

Talla

Rahoton da aka fitar yau Laraba ya ya yi nazari kan matasa masu shekaru 10 zuwa 19 daga sasan duniya daban daban, don duba matsalolin lafiyan da ke addabar su.
Rahoton ya rawaito jami’a mai kula da bangaren iyali mata da yara a hukumar ta WHO Flavia Bustreo, ma mai cewa al’umar duniya ba sa bai wa lamuran lafiyar matasa muhimmancin da ya dace.

Wani bangaren binciken kuma ya gano cewa rabin dukkan mutanen da ke samun matsalar tabin hankali, sun fara nuna alamu ne tun suna da shekaru 14 a duniya.
Don haka masanamn suka ce in har matasan da keda cutar tabin hankali sun sami kulawar da suke bukata, hakan zai iya rigakafin matsalolin da za su iya fadawa a wani lokaci cikin rayuwarsu.

Binciken ya duba matsalolin da ke addabar matasa da dama, da suka hada da shan taba sigari, barasa, amfani da miyagun kwayoyi HIV/AIDS, matsalolin da suka shafi kwakwalwa jima’I da sauransu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.