Amurka

Amurka ta lashi takobin ci gaba da jagorantar duniya

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Barak Obama ya kare matakan da kasar ke dauka kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen duniya. Shugaba Obama, da yi jawabi ga al‘ummar duniya, ya tabo muhimman batutuwan da suka shafi kasashe daban daban.

Talla

Cikin jawabin da ya yi a wata makarantar horon sojojin ta West Point, shugaban Obama ya kafe kan matakan da Amurka ke dauka a dangantakarta da sauran kasashen duniya.

Mr Obama yace Amurka zata jagoranci sauran kasashen duniya, amma bata hanyar shiga yaki ba tare da kwararan dalili ba, don haka sai yace abu mai muhimmanci ga kasar shine yadda take jagorantar sauran kasashen duniya.

Shugaban na Amurka ya kuma yi gargadin cewa kasasr shi, a shrye take ta mayar da marttani kan tsokanar da China ke wa makwabtanta a kan teku, ina yace duk inda wata kasa ke tsakana, ko dai a kudancin Ukraine ko kudancin tekun China, hakan zai iya sa a yi amfani da karfin soja.

Shugaban ya kuma lashi takobin kara tallafin da Amurka ke baiwa ‘yan tawayen da ke fada da gwamnatin shugaban Syria Bashar al-Assad, don su samu su tunkari abokan gabar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI