Amurka

Ana samun ci gaba a yaki da cutar Cancer

Hoton kwayar cutar Cancer ko Sankara
Hoton kwayar cutar Cancer ko Sankara (DR)

Kwararru masu bincike kan cutar Cancer ko sankara sun ce an sami gagarumin ci gaba a yakar cutar da ke sanadiyyar mutuwar fiye da mutane Miliyon 7 a kowace shekara a fadin duniya, sai dai rashin isassun kudade na matsayin babban kalu bale.Kwararru sun ce sanya mutane su ci abincin da ya dace, su motsa jiki sannan kuma su daina shan taba sigari na daga cikin matakan da zasu taimaka wajen hana kamuwa da wasu nau’oin cutar ta Cancer da dama.Sai dai kwararrun da ke taron su a kasar Amurka, sun ce har yanzu akwai wasu matakan da suka shafi muhalli da ake gani zasu iya jawo Cancer, da aka gagara warware su.