Spain

Juan Carlos na Spain ya yi murabus

Sarkin kasar Spain mai murabus, Juan Carlos
Sarkin kasar Spain mai murabus, Juan Carlos REUTERS/Oleg Popov/Files

Rahotanni daga kasar Spain sun ce Sarkin kasar Juan Carlos ya yi murabus daga mukaminsa inda ya mika ragamar mulki ga dansa Yarima Felipe, bayan kwashe shekaru kusan 40 yana shugabantar al’umar kasar. 

Talla

Dan shekaru 76, Sarki Carlos ya mika wasikar murabus dinsa ne ga Fira ministan kasar Mariano Rajoy a daidai lokacin da yake fuskantar suka kan zargin wasu daga cikin iyalansa da ake yi na hanu a wata badakalar kudade.

A rubutaccen jawabin ajiye mulkinsa da aka rabawa kafofin yada labarai, Carlos ya ce cike da alfahari da godiya ga irin goyon bayan da al’umar kasar suka bashi.

A cikin jawabin na shi Carlos ya kuma ce lokaci ya yi da zai mika ragamar mulki ga dansa wanda zai gaje shi, inda ya bayyana cewa matasa ne ya kamata su fara jagorantar tafiyar kasar.

“A yau matasa ne ya kamata su shige mana gaba a tafiyar da muke yi a matsayin mu na kasa.” Inji Carlos.

An dai nada Sarki Carlos ne a shekarar 1975 bayan da Janar Francisco Franco ya rasu.

Yanzu haka ya bayyana cewa Yarima Felipe dan shekaru 46 ne zai maye gurbinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.