Amurka

Obama ya soma ziyara a wasu kasashen duniya

obama
obama

Shugaban Amurka Barack Obama, ya isa birnin Warsaw ko kumaVarsovie fadar gwmanatin kasar Poland a matakin farko na ziyarar da za ta kai shi a kasashen da dama na duniya.

Talla

Bayanai na nuni da cewa a lokacin wannan ziyara ta birnin Warsaw, Obama zai gana da sabon shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko.

Wasu daga cikin kasashen da aka tsara Obama zai ziyarta sun hada da birnin Brussels na kasar Belgium domin taron kasashen duniya 7 masu karfin tattalin arziki bayan da aka dakatar da Rasha daga kungiyar.

Har ila yau Obama zai wuce zuwa Faransa domin halartar bukukuwan cika shekaru 70 da soojin kawance suka kaddamar da farmaki domi fatattakar sojojin kasar Jamus daga Faransa a lokacin Yakin Duniya na Biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI