Canada

Dan bindiga ya kashe ‘Yan sandan Canada uku

'Yan sandan kasar Canada suna aikin neman dan bindiga da ya kashe Jami'an tsaro uku
'Yan sandan kasar Canada suna aikin neman dan bindiga da ya kashe Jami'an tsaro uku REUTERS/Ron Ward/Moncton

Wani dan bindiga ya budewa ‘Yan sandan kasar Canada wuta inda ya kashe uku daga cikinsu tare da raunata wasu guda biyu, kamar yadda rundunar ‘Yan sandan kasar ta tabbatar. Al’amarin ya faru ne a Moncton a lardin Brunswick. Yanzu haka ‘Yan sandan sun ce suna neman dan bindigar da suka ce sunansa Justin Bourque dan shekaru 20. ‘Yan sandan kuma sun yi kira ga mutanen yankin su zauna a gida.