G7

Shugabannin G7 sun gargadi Putin na Rasha

Taron Shugabannin kasashe 7 masu karfin tattalin arzikin duniya
Taron Shugabannin kasashe 7 masu karfin tattalin arzikin duniya REUTERS/Yves Herman

Shugabannin manyan kasashen duniya nasu karfin tattalin arziki guda bakwai da ake kira G7, sun yi gargadi ga Shugaban Rasha Vladimir Putin akan ya kaucewa ruruta wutar rikicin kasar Ukraine ko kuma su tsaurara wa Rasha sabbin takunkumai.

Talla

Kasashen sun yi watsi da irin rawar da Rasha ke takawa a rikicin kasar Ukraine.
Wannan ne karon farko da aka gudanar da taron shugabannin na G7 ba tare da kasar Rasha bad a suka kora saboda ballewar yankin Crimea daga Ukraine suka ikonta.

A yau Alhamis ana sa ran kasashen zasu tattauna game da ci gaban tattalin arziki da wasu batutuwa da suka shafi ci gaba.

Wannan shi ne karon farko tun a shekarun 1990 da aka gudanar da taron na kasashen G7 ba tare da halartar Shugaba Vladimir Putin ba.

Kodayake shugabannin sun kara jaddada aniyarsu ta cewa kofa a bude take su tattauna da Putin, amma sun bayyana cewa akwai bukatar Putin ya amince da zaben da aka yi kasar Ukraine a watan da ya gabata, kamar yadda suka bayyana a wata sanarwa da suka fitar ta bai daya.

Shugabannin sun yi kara yin gargadi cewa ba za su zira ido suna kallo ana kara ruruta wutar kasar Ukraine ba, tare da yin kira da babbar murya da cewa ya zama dole a dakatar da yaduwar rikicin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.