Scotland-Libya

Dangin maharin Lockerbie sun fara yunkurin wanke shi

Marigayi Abdelbaset al-megrahi da aka zarga da harin Lockerbie
Marigayi Abdelbaset al-megrahi da aka zarga da harin Lockerbie Reuters

Dangin mutumin nan da aka yanke wa hukunci sakamakon samun shi da laifin dasa bom a jirgin da ya tarwatse a sararin samaniyan Lockerbie, a shekarar 1988 sun fara wani yunkuri don wanke she bayan mutuwarsa.

Talla

Abdel Basset al-Megrahi ne kadai mutumin da aka hukunta kan harin da aka kai wa jirgin saman mallakin kamfanin Pan Am, da mutane 270 da ke ciki duk suka mutu tare da wasu 11 a kasa.

A shekarar 2001 aka yanke wa Megrahi hukuncin daurin rai da rai, amma hukumomin Scotland suka sako shi a shekarar 2009, bayan da aka gano yana fama da cutar sankara ko Cancer a shekara ta 2012 da ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.