Amurka-Iran-Isra'ila

An bude taron tattaunawa tsakanin Iran da Amurka

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani REUTERS/Denis Balibouse

A yau litinin manyan jami’an kasar Iran da takwarorinsu na Amurka suka farazama kan teburin tattaunawa game da batun makamashin nukiliyan da kasar Iran din ke yunkurin mallaka. 

Talla

Taron wanda za a kwashe kwanaki biyu ana yinshi a birnin Geneva, ya kasance na farko tun bayan shekarun 1980’s da kasashen biyu suka zauna a teburin tattaunawa.

Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da aka tunkari wa’adin 20 ga watan Yuni da aka shata tsakanin kasashen yammci da kasar ta Iran a matsayin ranar da za a kulla yarjejeniya.

Jami’in dake wakiltar Iran a zantawar Abbas Araqchi ya bayyana a baya cewa tattaunawar da suka farad a kasar ta Amurka na da alaka da cewa akwai takunkumai da kasar Amurka ta kakabawa Iran.

Hukumomin Tehran da Washington sun kwashe shekaru da dama ba sa ga maciji tun bayan da aka yi juyin juya halin a kasar ta Iran lamarin da ya kai ga aka garkuwa da wasu ‘yan kasar Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.