Brazil 2014

Ana shirin fara wasanni a gasar cin kofin duniya a Brazil

Yau Alhamis ake fara wasannin gasar cin kofin duniya, da za a yi a kasar bazil, inda Brazil mai masukin baki zata yi wasan farko da Croatia. Sai dai yanzu haka cikunan ‘yan kasar ta Croatia sun gama durar ruwa, don kuwa da dama daga cikin ‘yan kasar suna tunanin a yau din kam sai dai buzun ‘yan kasar tasu.Wata jaridar kasar ta Croatia yace wannan shine wasa mafi girma da kasar zata taka.A wani bangaren kuma, kungiyar taraiyyar Turai ta EU ta kaddamar da wani gangamin da ke yaki da aikata masha’a da yara kanana, yayin wasan na cin kofin duniya, kuma tuni ‘yan wasan kasar ta Brazil kamar su Kaka da Juninho Pernambucano suka amince su bayar da goyon baya a wannan gangamin.Dama hukumomin kasar ta Brazil suna ta fargabar cewa wasu masu sha’awar wasan kwallon kafa daza su je kasar, zasu kuma nemi jin yadda harkar nisha da ake ta dangantawa da kasar, take gudana.sai dai har yanzu rahotannin na cewa ana ci gaba da samun zanga zanga a wasu sassan Brazil din, inda wasu ‘yan kasar ke ci gaba da adawa da daukar nauyin gasar da kasar tasu tayi, ganin yadda suka ce an kashe makudan kudaden talakawa, ba gaira ba dalili.Rahotannin na cewa yau Alhamis, sai da ‘yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye, da harba harsashin roba, kan wasu masu zanga zangar a birninSao Paulo.Ma’aikatan filin jirgin saman birnin Rio de Janeiro sun rufe hanyoyin da ke isa filin jirgin, a ci gaba da zanga zangar da suke yi.