Amurka-Taliban

Hagel ya kare matakin yin musayar Fursunoni da Taliban

Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel
Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel Reuters

Sakataren Tsaron Amurka, Chuck Hagel ya kare matakin da gwamnatin su ta dauka na musayar wasu Yan kungiyar Taliban da sojin kasar guda, wanda ya haifar da cece kuce a cikin kasar. Yayin da ya ke kare sukar da Yan Majalisar kadsar ke yi masa, Hagel yace shugaba Obama ya dauki matakin ne dan ceto ran sojin kasar, kuma matakin bai sabawa doka ba.

Talla

‘Yan Majalisar daga Jam’iyar Republican na kallon musayar a matsayin kuskure, amma Hagel yace musayar ta zama dole domin samun ‘yan Sojan mai suna Sergeant Bowe Bergdahl.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.