Iraqi-Amurka

Amurka na shirin taimakon Iraki ta yaki 'yan tawayen dake arewacin kasar

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque

Yayinda mayakan ‘yan jihadin kasar Iraqi ke ci gaba da tunkarar birnin Baghadaza, Amuraka tace tana tunanin daukar dukkan matakan da suka dace, don taimakawa gwamnatin kasar. Tuni kamfanonin Amurka suka fara kwashe daruruwan ma’aikatansu, daga yankunan da tashe tashe hankulan da ke faruwa.Mayakan kurdawan sun karbe birnin Kirkuk na arewacin kasar, da aka raba shi tsakanin kabilu, da kuma suka shafe shekaru da dama suna kokarin mulkarshi, duk da adawa da hakan, da gwamnatocin kasar da suka shude suka yi ta nunawa.Ministan harkokin wajen kasar ta Iraqi Hosyhar Zebari, ya tabbatar da cewa dakarun kasar da Amurka ta kashe makudan kudade wajen basu horo da kayan aiki, kafin ta janye sojanta daga kasar a shekarar 2011, sun narke.Shugaba Obama yace Iraki zata bukaci agaji daga Amurka dama sauran kasashen duniya.Mr Obama ya kara da cewa rundunar tsaron kasar na duba dukkan abubuwan da suyka dace ayi, don haka a cewar shi komai na iya faruwa.A wani abu na ba sabunba, wannan karon hukumomin birnin Washington na tare da Iran, da suka dade suna gaba, inda dukkan su ke nuna damuwa da yadda ‘yan sunni ke ci gaba da yakar dakarun gwamatin Iraqi.Zuwa yanzu a kalla mutane rabin miliyon ne suka tsere wa yakin da ake yi, kuma hukumar samar da abinci ta MDD tace ta fara samar da tallafi ga mutane dubu 42, dake matukar bukata.