Mexico-Amurka

Amurka ta mika yara kanana 'yan gudun hijira 6,000 zuwa Mexico

Wasu 'yan gudun hijira tare da 'ya 'yansu
Wasu 'yan gudun hijira tare da 'ya 'yansu REUTERS/Antonio Parrinello

Fiye da yara kanan dubu 6 ‘yan kasar Mexico aka mayar gida, a lokacin da suka yi yunkurin tsallakawa zuwa Amurka, ta barauniyar hanya, cikin wata hudun farkon wannan shekarar. Jami’an gwamnatin Mexico, da suka fidda wadannan alkaluman sun ce, kusan dukan wadanda aka kama a wannan lokacin, ba shine farkon yunkurinsu na tsallakawa zuwa Amurka ba. Yara suna shiga hadari, tare da tafiyar daruruwan Km su kadai, don kaucewa matsanancin halin tattalin arziki, da kuma tashe tashen halula a kasashen su.