Cuba-Venezuela

Cuba ta nemi a taimakawa Venezuela ta kawo karshen bore da ake yi a kasar

Shugaban kasar Cuba, Raul Castro
Shugaban kasar Cuba, Raul Castro REUTERS/Grigory Dukor

Shugaban Cuba Raul Castro ya nemi kawayen kasar su bayar da tallafi ga hukumomin kasar Venezuela, da ke fama da bore daga masu adawa da gwamnati. Castro mai shekaru 83 a duniya, da ke jawabi a kasar China, yace wasu tsiraru da suka gagara hambarar da marigayi Hugo Chavez, sun koma suna neman kifar da gwamnatin Nicolas Moduro.Kasashen 2 suna matukar aminci da juna, kuma tattalin arzikin kasar Cuba ya dogara ne kan Venezuela, da ke samar mata man fetur cikin farashi mai sauki.