Iraqi-Amurka

Ana ci gaba da arangama tsakanin dakarun Iraqi da mayakan sa kai

Mayakan Iraqi suna harba makamai kan yankunan da mayakan sa kai suka karbe
Mayakan Iraqi suna harba makamai kan yankunan da mayakan sa kai suka karbe Reuters/路透社

Dakarun kasar Iraqi na ci gaba da arangama da mayakan sa kai a yunkurin da bangarorin biyu ke yi na ganin sun mallake wani garin mabiya akidar Shi’a dake arewacin kasar, lamarin da ya sa mafi yawan mazauna garin suka fice domin neman mafaka.

Talla

Wannan kuma na faruwa ne a dai dai lokacin da kasar Amurka ke duba yiwuwar yin amfani da jirge mara matuki domin kai hare hare kan mayakan dake tada kayar baya.

Shugaba Barack Obama a jiya lahadi ya ce Amurka ba za ta aika da dakarunta zuwa kasar ba, bayan da ‘yan jam’iyar Republic suka nuna matsin lamba kana gazawar gwamnati na kare aukuwar wannan rikici.

Yanzu haka Sakataren harkokin wajen kaxar Amurka John Kerry ya ce Amurka na kuma duba yiwuwar hada kai da kasar Iran domi ganin an shawo kan rikicin wanda aka kwashe mako daya ana yi.

A fadan an baya bayan nan, rahotanni sun ce mayakan na sa kai sun karbe wasu anguwanni da dama dake garin Tal Afar, wanda mabiya akidar Shi’a suke da rinjaye.

Har ila yau mayakan sun karbe yankunan Al – Adhim da Diyala dake arewacin Bagadaza, babban birnin kasar ta Iraqi.

A jiya lahadi adkarun kasar sun yi ikrarin kashe akalla mayakan 300 a wata arangama da suka yi bayan da dakarun Kurdawa suka sa hanu a fadan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.