Masar

Sabon shugaba na cika alkawarin murkushe ‘yan uwa musulmi a Masar

Seoudi supermarket

Hukumomi a Kasar Masar sun kwace shaguna mallakar kungiyar ‘Yan uwa Musulmi, a ci gaba da aiwatar da alkawarin da shugaban kasa Abdel Fatah al Sisi yayi na murkushe kungiyar da ma duk mai goyon bayanta

Talla

Shugaban Yan Sandan Birnin Alkahira, Bri Janar Ali al Demerdash, ya ce an rufe shagunan Seodi da na Zad Store mallakar shugabanin kungiyar ‘yan Uwa Musulmi da ke a kasar ta Masar.

Shagudan talata Hajoji na Seodi dai manyan shaguna ne mallakar Abdulrahman Seodi hamshakin dan kasuwa a kasar Masar da kuma ke da manyan Kantuna a kusan ko’ina a cikin kasar.

Yanzu dai Gwamnatin Abdel Fatah al-Sisi ta kwace daukacin kadarorin da ya mallaka, kawai domin yana goyon bayan Jam’iyyar ‘yan Uwa Musulmi ta hambararen shugaba Muhammad Morsi.

Dama dai wata Kotu a cikin watan Satumba Masar ta haramta dukkanin ayyukan kungiyar da kuma bada umurnin kwace kadarorin ta, abinda ya kai ga kwace hatta Masana’antu da Makarantun magoya bayanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.