Iraq

Tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan makomar Iraqi

Dakarun kasar Iraqi a garin Musul.
Dakarun kasar Iraqi a garin Musul. REUTERS/Stringer

Mayakan jihadi a kasar Iraki sun kwace karin wasu yankuna a wani muhimmin gari dake arewa maso yammacin kasar.Al’amarin da yayi sanadiyar kara samar da yan gudun hijira da ke kauracewa gidajen su.

Talla

kasar Amaruka ta bayyana aniyarta na yi yiwar amfani da jiragen yaki marar matuki, domin taimakawa gwamnatin kasar ta Iraki wajen yakin da ‘yan tawayen.

Wannan matsayin na Amurka ya nuna yadda gwamnatin Obama ta kauce daga matsayin da ta dauka tun farko, inda sakataren harkokin wajen Amurkan John Kerry yace suna duba yiyuwar daukar matakan soja tare da Iran, don yakar mayakan jihadi a Iraqi.

A makon daya gabata ne dai, mayakan jahadin dake kokarin kafa gwamnatin musulunci a kasar Iraqi, da kuma ke samun taimakon magoya bayan tsohon shugaban kasar marigayi Saddam Hussein suka kwace Garin Musul gari na biyu mafi girma a kasar, da kuma wani babban yanki a Ninive de ke arewaci, sai kuma Tikrit mahaifar Marigayi Saddam Husaini da wasu yankuna na Salaheddine, Diyala a gabashi sai Kirkouk dake a arewacin kasar .

Kasashen Iran da Amuka, suna da manufarsu daban daban don ganin Iraqi ta murkushe ‘yan tawayen, da dake samun goyon bayan kungiyar Al-Qaeda.

Amaruka ta aike da dakarun zuwa Birni Bagdaza domin kare ma'aikantan ofishin jakandanci ta dake Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.