Iraqi-Amurka

Iraqi ta kori manyan jami’an tsaronta

Fira Ministan kasar Iraqi, Nuri al Maliki
Fira Ministan kasar Iraqi, Nuri al Maliki AFP PHOTO / Ahmed Saad / POOL

Gwamnatin kasar Iraqi, ta sallami wasu daga cikin manyan jami’an tsaronta, saboda gazawa da suka yi na dakile yunkurin da mayakan sa kai ke yi na karatowa birinin Bagadaza. Wannan kuma na faruwa ne a dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yiwuwar rabewar kasar saboda wannan rikici.

Talla

Tuni kasar Amurka ta kara tura dakaru 275 domin tsaurara maatkan tsaro a ofishin jakadancinta yayin da take duna yiwuwar kai hare hare ta sama kan mayakan jihadi na kungiyar ISIL dake samun goyon bayan ‘yan Sunni.

An kwashe fiye da mako guda ana arangama tsakanin dakarun kasar da mayakan, lamarin da ya sa Fira Minista Nuri al Maliki ya sallami manyan jami’an tsaron kasar ciki har da mai kula da garin Nineveh dake Arewacin kasar.

Wannan kora ta biyo bayan bayanai dake nuna cewa dayawa daga cikin dakarun kasar sun arce a lokacin da mayakan suka mamaye garin Nineveh mai dauke da mutane miliyan biyu.

Har ila yau rahotanni na nuna cewa an tsinci gawawwakin wasu sojoji 18 a garin Samarra, wadanda aka harbe su a ka da kirji.

Rahotanni na nuna cewa a jiya Talata, mayakan sun karbe wasu yankuna dake Baquba, garin dake da tazarar kilomita 60 daga birnin Bagadaza.

Wannan kuma shine babban kusanci da mayakan suka kai ga babban birnin na Bagadaza.

A farkon makon nan, dakarun kasar ta Iraqi sun yi ikrarin hallaka mayaka kusan 300.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.