Jamus

An ceto wani Bajamushe da ya makale a rame

Masu aikin ceto sun tsamo Johann Westhauser wani Bajamushe da ya makale a cikin wani rame mai zurfi a tsaunin yankin Alps
Masu aikin ceto sun tsamo Johann Westhauser wani Bajamushe da ya makale a cikin wani rame mai zurfi a tsaunin yankin Alps REUTERS/Bergwacht

Masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da wani Bajamushe da ya makale cikin rame tsawon kwanaki 11 a tsaunin Alps. Yanzu haka mutumin mai suna Johann Westhauser ana kula da lafiyarsa kafin isa da shi zuwa Asibiti.

Talla

Mutumin mai shekaru 52 ya makale ne a cikin wani kogo da aka auna zurfinsa ya kai kimanin mita 1,000. Rahotanni sun ce ya samu rauni da yawa a kansa.

Kwararru daga kasashen Jamus da Austria da Italiya da Switzerland da Croatia suka hada kai domin kubutar da Bajamushen wanda ya kwashe kwanaki 11 a karkashin kasa.

Johann Westhauser ya makale ne a cikin kogon a ranar 8 ga watan Yuni a lokacin da ya ke gudanar da wani bincike tare da wasu mutane guda biyu, wadanda cikinsu ne wani ya bayar da sanarwar ya makale a karkashin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.