Majalisar Dinkin Duniya

MDD - 20 ga Watan Yuni ce ranar ‘yan gudun hijira ta Duniya

informafrica.com

Yau Jumu’a 20 ga Watan Yuni ce ranar da Majalisar dunkin Duniya ta kebe domin lura da matsalolin ‘yan gudun hijra a dukkanin fadin Duniya. Yanzu haka kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar, ta fitar da alkalumman da suka ce kimanin ‘Yan gudun hijira miliyan 52 da dubu 200 ne suka kaurace wa gidajensu a shekarar 2013 kawai

Talla

Hukumar ta yi kira ga manyan kasashen Duniya da su taimaka a kawo karshen tashin hankalin da ake samu a wasu kasashen Duniya.

Rahotannin da ke ci gaba da fitowa na bayyana cewar tashin hankalin kasar Siriya ne kan gaba wajen yawaita ‘yan gudun hijira a Duniya.

Tun bayan soma tashin hankalin a Watan Maris na 2011 akalla mutane Miliyan 2 da rabi ne suka bar gidajensu a Siriya a yayin da wasu Miliyan 6 da rabi kuma ba’a san inda suke ba.

Majalisar dunkin Duniyar ta kuma bayyana cewar wasu tashe-tashen hankullan da ke faruwa a kasashen Jamhuriyar Afruka ta tsakiya da Sudan ta Kudu ma na kara yawan ‘yan gudun hijirar.

Ko a yau ma Kungiyar Likitocin da basu da sanke na Majalisar dunkin Duniya wato Doctors without borders ta fidda rahoton yanda ake dada samun mutuwar ‘yan gudun hijira musamman kananan Yara ‘yan kasa da shekaru 5 a sansanonin ‘yan gudun hijirar da Majalisar dunkin Duniya ke kulawa da su a kasar Sudan ta kudu.

Inji rahoton wannan na faruwa ne sakamakon yanda Sansanonin ke dada lalacewa ta fanning muhallin da ‘yan gudun hijirar ke zaune, da kuma tsananin Yunwa da ke addabar mutanen da fada ya kora daga gidajensu a Sudan ta Kudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.