MDD

‘Yan gudun hijira sun haura miliyan 50 a duniya

'Yan gudun hijira a kasar Jamhuriyar demokuradiyar Congo
'Yan gudun hijira a kasar Jamhuriyar demokuradiyar Congo Reuters

Majalisar Dinkin Duniya tace adadin ‘Yan gudun hijira da suka kauracewa gidajensu saboda rikici da yake-yake sun haura miliyan 50 a 2013, adadi mafi yawa tun yakin duniya na biyu. Kuma kasar Syria ce ta fi kowace kasa a duniya yawan ‘yan gudun hijira.

Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta fitar da alkalumman da suka ce kimanin ‘Yan gudun hijira miliyan 52.2 suka kauracewa gidajensu a 2013.

A bara kawai an samu karin ‘Yan gudun hijira sama da Miliyan shida, kuma adadin ya karu ne saboda rikicin Syria.

Kimanin ‘Yan gudu hijira miliyan biyu da rabi ne suka fice daga Syria tun barkewar rikicin kasar a watan Maris na 2011.

Akwai dimbin mutane da suka yi gudun hijira daga gidajensu saboda rikice rikicen da ake yi a kasashen Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Sudan ta kudu.

Hukumar ta yi kira ga manyan kasashen duniya su taimaka a kawo karshen tashin hankalin da ake samu a wasu kasashen duniya.

Hukumar tace adadin 'Yan gudun hijira a kasashen Afrika da ke kudu da Sahara ya kai Miliyan 2.9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.