Australia

Australia zata bayar da kudi ga masu neman mafaka da suka amince su koma kasashensu

Wasu masu neman mafaka da suka isa kasar Italiya
Wasu masu neman mafaka da suka isa kasar Italiya REUTERS/Antonio Parrinello

Hukumomin kasar Australia sun yi tayin bayar da kudaden da suka kai Dalar Amurka dubu 10, ga duk masu neman mafaka, dake sansanin da ake tsare da su, da kuma ya amince ya koma kasar shi ta asali.Sai dai wannan tayin ya jawo suka daga kungiyoyin dake rajin kare hakkokin ‘yan gudun hijiran a sassan duniya.A ‘yan shekarun nan Australia ta kara tsaurara dokokinta na bayar da mafaka, inda ake hana wa wadanda suka isa kasar cikin kwale kwalen da basu cika ka’ida ba sauka a kasar, koda kuwa sun cika ka’idojin samun mafaka.