Brazil

Dilma Roussef ta bayyana aniyar takarar shugabancin Brazil

Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef tare da tsohon shugaba, Luis Inacio Lula da Silva
Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef tare da tsohon shugaba, Luis Inacio Lula da Silva REUTERS/Joedson Alves

Shugabar Kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana aniyar ta, ta yin takarar shugabancin kasar a karo na 2. Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ta nuna yadda ‘yan kasar suka amince da takarar taka, duk da tashe tashen hankulan da aka samu sakamakon daukar nayin gasar cin kofin duniya da kasar ke yi.Jam’iyya PT ta Rousseff ta amince da takarar shugabar, a lokacin da aka yi babban taron jama’iyyar a birnin Brasilia, inda tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva ya sami halarta.